Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:10:08    
Mutane da yawa suna mai da hankulansu sosai kan nakasassu

cri

Malama Hu Yi Ling ta kamfanin Siemens ta gaya wa wakiliyarmu cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 125 da kafa rukunin kara karfin kunne na kamfanin Siemens, tun daga shekarar 1897, kamfanin nan ya fara bincike da kera kayayyakin ba da taimako ga kurame, daga shekarar 1996 ya zuba jari a kasar Sin don gina ma'aikatun fitar da injunan kara karfin kunne wajen sauraro, wato audiphone. Malama ta ci gaba da cewa, babban makasudin shiga bikin nan shi ne don gabatar wa kasar Sin da wasu fasahohin ba da taimako ga kurame a daidai lokaci, ta yadda sha'anin mayar da karfin kunne na kasar Sin zai ci gaba tare da na kasashen waje.

Wani shugaban tashar samar wa nakasassu kayayyakin taimako na birnin Su Zhou na lardin Anhui na kasar Sin malam Hou Xiang Shan ya yi aikin sayen kayayyakin nakasassu har shekaru fiye da goma, a wannan gami, musamman ne ya je bikin baje koli, ya dudduba sababbin kayayyakin musamman na zamani sosai. Ya bayyana cewa, kayayyakin zamani sosai sun rage wahalolin da nakasassu suke sha, alal misali, a da, ana amfani da kujerun guragu da karfin mutane,amma yanzu ana amfani da su da karfin lantarki tare da cajinsu da fasahar zamani, shi ya sa an rage amfani da karfin mutane. Ya ji ya sami fasahohi da yawa a gun bikin baje kolin nan, kuma ya yi shirin sayen wasu kayayyakin da aka nuna.


1 2 3