Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:10:08    
Mutane da yawa suna mai da hankulansu sosai kan nakasassu

cri
 

A gaban dandalin nune-nune na madaba'ar yin littattafan makafi, mutane masu yawan gaske sun taru har ya sa wurin ya cunkushe. Tsarin injuna masu kwakwalwa da aka kafa domin amfanawa makafi wanda madaba'ar yin littattafan makafi ta birnin Beijing da cibiyar kimiyya ta kasar Sin suka yi nazari da kerawa cikin hadin guiwa ya jawo sha'awar mutane sosai da sosai. Malam He Chuan wanda ke da shekaru 30 da haihuwa yana daya daga cikin wadanda suka tsara fasalin abubuwan ba da bayannoni wato software, kuma shi makaho ne. Ya gaya wa wakiliyarmu cewa, daga tushe ne wannan software ya daidaita matsalolin nakasassu wajen yin rubutu da karatu da aikawa da E-mail da sauran matsalolinsu ta hanyar Kumputer, har ma nakasassu suna iya kula da harkokin tashoshin internet, Makafi za su iya aiwatar da kome da kome tamkar yadda kowa yake yi ta hanyar kumputer.

Sa'anan kuma malam He Chuan ya gaya wa wakiliyarmu cewa, a cikin wasu sa'o'I kawai, an bayar da dukkan abubuwa dangane da wannan software da aka shirya, kuma a wurin, wasu 'yan kallo sun yi farin ciki da gwajin amfani da su, kuma nan da nan suka yi kwangilar sayen wannan software.

Kayayyakin da shahararrun masana'antun kasashen waje suka fitar kuma bikin baje kolin nan ya nuna su ba ma kawai sun wadatar da kasuwannin sayar da kayayyakin nakasassu na kasar Sin ba, hatta ma ya kawo fasahohin zamani sosai daga kasashen waje.


1 2 3