Malam Liu ya kara da cewa, kasar Sin za ta tsananta yanke hukunci kan wadanda ke amfani da magani mai sa kuzari, za ta kuma inganta fadakar da mutane da yaki da magani mai sa kuzari, kazalika kuma, za ta kara karfin binciken ko 'yan wasan Sin suna yin amfani da magani mai sa kuzari, ko a'a.
Ran 20 ga wata, a nan Beijing, Wang Gang, mataimakin darektan ofishin kula da ayyukan gine-gine domin gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, ana gina muhimmin filin wasa na gasar wasannin Olympic ta Beijing, wato filin wasan kasar Sin ko kuma Bird's Nest a Turance, kamar yadda ya kamata. An kiyasta cewa, za a kammala aikin a watan Afrilu na wannan shekara.
Wannan jami'i ya yi karin bayani da cewa, yanzu, ban da filin wasa na Bird's Nest, an gama ginawa da kuma yin kwaskwarima kan filaye da dakunan wasa 31 da dakunan aikin horaswa 45 da za a yi amfani da su a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. Nan gaba za a ci gaba da jarraba su ta hanyar shirya gasanni.(Tasallah) 1 2 3
|