Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 14:37:58    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(20/03-26/03)

cri

Bayan da aka kunna wutar yolar, daga baya an fara mika ta a doron kasar Girka har na tsawon sati guda. Tsawon hanyar da za a bi a Girka wajen mika wutar yolar gasar wasannin Olympic ta Beijing zai kai misalin kilomita 1528, za a ratsa yankuna 16 da birane 43 na Girka, sa'an nan kuma, za a shirya bikin mika wutar yolar a cikin wasu 29 daga cikin wadannan birane 43. Masu rike da wutar yola 605 za su mika wutar yola a cikin Girka. Ran 30 ga wata, wutar yolar za ta isa filin wasa na Panathinaiko da ke cibiyar birnin Athens, inda aka yi gasar wasannin Olympic ta zamani a karo na farko a shekarar 1896. Kwamitin wasannin Olympic ta Girka zai mika wa kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing wutar yolar a wannan filin wasa.

Ran 24 ga wata, a nan Beijing, Liu Peng, shugaban hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa, hukumarsa za ta kafa kungiyar sa ido kan yin amfani da magani mai sa kuzari, domin tabbatar da ganin cewa, 'yan wasan Sin za su shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing ba tare da yin amfani da magani mai sa kuzari ba.


1 2 3