
Baya ga tsare-tsaren gine-gine, Dalian ta fi dora muhimmanci kan launukan gine-ginenta, ta haka dukan birnin na da kyan gani sosai domin launuka daban daban.
Kazalika kuma motoci su ma suna jawo hankulan mutane a Dalian. An shafa zane-zane masu launuka daban daban a jikunan motocin al'umma, har ma sun yi kama da dakunan nuna zane-zane da suke iya tafiya.
Ko da yake ba safai a kan iya ganin dimbin kekuna a yankin tsakiya na Dalian ba, amma ana iya ganin masu yawon shakatawa suna hawan kekunan musamman a babban fili a kusa da teku da a kan hanyoyin mota. Suna farin ciki sosai saboda yin yawo tare da kallon sararin sama mai launin shudi da teku da kuma filayen ciyayi.
Yanzu Dalian ta kan sifanta kanta da 'birni na soyayya' a lokacin da take dukufa wajen yada aikin yawon shakatawa nata a gida da kuma a ketare. 1 2 3
|