Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 16:41:40    
Birnin Dalian, birni ne na soyayya

cri
 

Tare da kiyaye al'adun gargajiya na kasar Sin, Dalian tana koyi da abubuwan fifiko da kasashen yammacin duniya suke nunawa a fannin zayyana lambu. Ta dasa itatuwa da ciyayi iri daban daban bisa matakai daban daban ta hanyoyi daban daban. Filayen ciyayi sun sami rinjaye a wuraren yawon shakatawa da manyan filaye, sa'an nan kuma, an dasa dogayen itatuwa da dimbin furanni a cikinsu, ta haka ana iya ganin kyawawan lambunan zamani da yawa a birnin Dalian.

Yanzu akwai manyan filaye 48 a Dalian. Dalian na matsayin daya daga cikin biranen kasar Sin da suka fi mallakar manyan filaye. Ko da yake wadannan manyan filaye sun sha banban da juna sosai, amma dukansu sun sanya masu yawon shakatawa suna mantawa da komawa gida.

A shekarun baya, gine-ginen da aka samu a Dalian ya kara samun kyan gani. Gine-gine irin na salon Gothic da na salon Rome a kewayen babban filin Zhongshan sun zama kyan karkara a idon mutane. Haka kuma tituna masu nuna sigar musamman ta kasar Rasha da kasar Japan da aka kammala yi musu kwaskwarima a kwanan baya ba da dadewa ba sun samar da yanayin musamman na kasashen ketare a wannan birni na zamani.


1 2 3