Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 21:35:30    
An kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing

cri

A gun bikin kuna wutar yola, Liu Qi, shugaban hukumar kula da shirya wasannin Olympic ta Beijing ya ba da jawabi cewa, "ina yi wa jama'ar kasar Girka da gwamnatinta godiya sabo da goyon baya da taimakon da suka nuna wa wasannin Olympic na Beijing. A karkashin jagorancin wutar yola ta wasannin Olympic, kuma bisa kokarin da jama'ar Sin da ta suran kasashen duniya daban daban ke yi, za mu shirya wasannin Olympic na Beijing wadanda ke da sigar musamman kuma bisa babban matsayi. Muna fatan wutar yola ta Olympic za ta haskaka a cikin zukatan jama'a har abada, kuma za ta haskaka hanyar da bil-adam ke bi don neman zaman lafiya da aminci da ci gaba har abada."

Bayan da aka sami nasarar kunna wutar yola, babbar fada Maria Nafpliotou ya gaya wa mai ba da yolar cikin tsohon harshen Girka cewa, "ka jeka ka gaya wa mutanen dukkan duniya cewa, wasannin Olympic ke kusantowa cikin sauri! "(Halilu)


1 2 3