Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 21:35:30    
An kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing

cri
 

A gun bikin kuna wutar yolar da aka shirya a yau, a farkon farko, Minos Kyriakou, shugaban hukumar wasannin Oympic ta Girka ya ba da jawabi cewa, "yana fatan wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 za ta yadada manufar Olympic da darajar wasannin motsa jiki a wurare mafiya yawa na duniya, kuma yana fatan wasannin Olympic na karo na 29 zai sami cikakkiyar nasara."

Wutar yola ta wasannin Olympic ta zama alama ce ga zaman lafiyar duniya da amincinta wadanda jama'ar kasashe daban daban da masu harsuna daban daban, da masu bin addinai daban daban da kuma kabilu daban daban ke nemawa. A gun bikin kunna wutar yola, Jacques Rogge, shugaban hukumar wasannin Olympic ta duniya ya bayyana cewa, "a nan da zuciya daya, nake fatan kowa da kowa zai iya fahimtar abin da wutar yola ke nuna, a dukkan wuraren da yolar ta isa, za ta kawo wa jama'a labarin aminci da zaman lafiya, da ba da kwarin gwiwa ga jama'a da su kara neman samun kyakkyawar makomarsu. Dale ne, a yi wasannin Olympic da ba da yolar cikin zaman lafiya. Yolar wasannin Olympic tana hadin kan dukkan 'yan wasanni da mutanen duniya gaba daya, kuma yana hadin kanmu da ke amincewa da darikar Olympic da manufar wasannin motsa jiki. Yola za ta iya hadin kan jama'a, kuma za ta iya wakiltar zaman jituwa."


1 2 3