Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 21:35:30    
An kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing

cri

Yau 24 ga wata, a Olympia na kasar Girka, an kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, kana an soma ba da yolar wasannin Olympic na Beijing. Yau da misalin karfe 11 da rabi, agogon Girka, wato yayin da amon ganga ke tashi, an yi bikin kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing a bakin dakin Ibada na Hera, tsohon wurin Olympia. Fada mata 20 masu sanye da dogayen sket masu launin fari wadanda suka kasu cikin lauyuka biyu, suna tafiya daya bayan daya a tsakanin gishikan dakin Ibadan zuwa bakinsa, inda suka yi da'ira. Bayan haka babbar fada Maria Nafpliotou wadda ke dauke da tukunyar wuta a hannayenta, ta tafi daga dakin ibadan zuwa tsakiyar dandamalin ibadan, da babbar murya ta karanta jawabin yabon Apollo, mala'ikan rana.

Bayan da ta gama karatunta. Babbar fada Maria Nafpliotou ta ajiye wata yola a wurin inda karfin hasken ranar da mudubi ke tattare a bakin dandamalin Ibadan, don kunna wutar yola. Wannan ya alamanta cewa, an riga an sami nasarar kunna wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing. A cikin kwanaki 130 masu zuwa, masu ba da yola sama da dubu 20 wadanda suka zo daga kasashe da yankuna daban daban za su ba da yolar wasannin Olympic na Beijing a nahiyoyin duniya biyar don kawo wa duk duniya zaman lafiya da aminci da fara'a. A daren ran 8 ga watan Agusta mai zuwa, yolar za ta isa wurin da za a shirya bikin bude wasannin Olympic na Beijing don kunna wutar babbar yola ta wasannin Olympic na Beijing.


1 2 3