Bisa koyarwar da malamai masu fasahar aikin gona na kasar Sin suka yi cikin natsuwa, wadannan ma'aikatan Darfur suka gwanance wajen fasahar shuka kayan lambu da sauri. Ban da wannan kuma sun iya magana da Sinanci kadan sabo mu'amalar da ake yi tsakaninsu da aminai Sinawa, har sun iya ambata wasu sunayen kayan lambu da Sinanci.
"Alayyaho, tafarnuwa, ganye mai ba da mai, gurji."
Tsoho Fan ya bayyana cewa, wadannan ma'aikata sun yi aiki cikin sa'o'i 7 da rabi a kowace rana, yawan albashinsu kuma wajen dala 170 ne a kowane wata, sukan aika da kudin zuwa gidajensu da ke jihar Darfur. To, ta yaya wadannan ma'aikatan Darfur suke jinjina ga mai gidansu? Mr. Abudulla ya ce,
"Yana da kirki sosai, kuma yana kulawa da mu sosai."
Amma ta yaya mai gida Basine yake jinjina ma'aikatansa? Tsoho Fan ya ce,
"Suna aiki cikin natsuwa, idan ka nuna musu hanyar da za a bi wajen aiki, sai su san yadda za su gudanar da aikin su da kansu."(Umaru) 1 2 3
|