Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 20:15:00    
Ma'aikatan Darfur da ke gandun noma na kasar Sin da ke birnin Khartoum

cri

A hakika irin wannan gandun moma na kasar Sin ba daya kawai ba a birnin Khartoum, amma bambancin da ke tsakanin gandun noma na Lao Fan da sauran gandaye shi ne, ma'aikatan da aka yi hayarsu a gandunsa dukkansu sun zo ne daga shiyyar Darfur.

Yanzu yawan ma'aikatan Darfur da ake hayarsu a wannan gandun noma ya kai fiye da 20. Yayin da tsoho Fan ya tabo magana kan dalilin da ya sa ya yi hayar mutanen Darfur musamman shi ne, sabo da wadannan mutane ba su da zurfin ilmi, shi ya sa da wuyar samun aikin yi, sabo da haha yana son ba su hannu. Ya ce,

"Suna da kirki, halin da suke ciki wajen zama da abinci ba na a zo a gani ba ne, kuma ba su iya samun aikin yi ba sabo da ba su da ilmi da fasaha."

Muhimman ayyukan da wadannan ma'aikatan Darfur ke yi cikin gandun moma na tsoho Fan su ne, cire hakukuwa a gindin shuka, da ban ruwa ga gonaki da sauran ayyukan gona. Mr. Abudulla wanda yake da shekaru 40 da haihuwa wanda kuma ya zo ne daga lardin yammacin Darfur yanzu ya riga ya kware wajen aikin gandun. Ya ce,

"Aikina shi ne yin amfani da igiya don daure 'ya'yan soso a kan tanka, ta yadda za su hau sama sannu-sannu."


1 2 3