A karkarar birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan, da akwai wani gandun noma wanda Sinawa suka bude, ma'aikatan kasar Sudan da aka yi hayarsu cikin gandun dukkansu sun zo ne daga shiyyar Darfur. Sun ciyar da iyalansu ta hanyar aiki, sa'an nan kuma sun ba da taimako ga bunkasuwar wannan gandun noma. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilanmu suka ruwaito mana daga birnin Khartoum.
Bayan da aka shiga cikin gandun noma, kamar a shiga cikin wani karamin kauye na kasar Sin, ga kuke-kuken karnuka da na tsuntsaye, ga kuma itatuwa ko'ina, kuma ana iya ganin ganyayen lambu masu tsanwa shur suna girma da kyau cikin gonaki. Mai gandun noma Mr. Fan Chuanzhao shi ne ya karbe wakilanmu, ya ce,
"Fadin gangun noma ya kai misalin kadada 10, musamman domin shuka kayan lambu na kasa Sin, nau'orinsu kuma har da lafsur da ganye mai ba da mai da kabeji da alayyaho."
1 2 3
|