Da aka tabo magana kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, minista Yang ya ce,
'Kasar Sin ta zama tsohuwar kawa ta jama'ar kasashen Afirka. Har kullum muna ganin cewa, ko da yake moriyar da ke tsakanin kasa da kasa tana da muhimmanci, amma zumunci da da'a suna da muhimmanci sosai da sosai.'
A shekarar 2008, kasar Sin za ta shirya gasar wasannin Olympics. Wasu manema labaru sun gabatar da tambayoyi cewa, wasu mutane sun hada gasa wasannin Olympics da siyasa. Game da haka, minista Yang ya ce,
'Kaunar kasa, ba ta da nasaba da yunkurin mayar da gasar wasannin Olympics a siyasance. Duk wadanda suke dubu abubuwa bisa matsayin adalci da gaskiya suna iya ganin cewa, jama'ar kasar Sin suna nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics cikin sahihiyar zuciya.'
1 2 3
|