Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 17:38:24    
Taron manema labaru na ministan harkokin waje na kasar Sin Mr Yang Jiechi

cri

A lokacin da ake shirya tarurrukan shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa a kasar Sin, taron manema labaru na ministan harkokin waje yana jawo hankulan jama'a sosai. Da karfe 10 na safe na ran 12 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Mr Yang Jiechi ya shirya taron manema labaru a zaure mai launin zinariya na hawa na uku na babban zauren jama'ar kasar Sin, inda ya bayyana kan manufofin diplomasiyya na kasar Sin.

A gun taron manema labaru, minista Yang ya amsa tambayoyi daga maname labaru 13 na gida da na waje. A cikin wadannan tambayoyi, dangantakar da ke tsakanin Sin Amurka ta fi jawo hankulan jama'a. Game da haka, minista Yang ya ce,

'A takaice dai, dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka tana kiyaye zaman karko, kuma tana ci gaba da samun bunkasuwa. Bangarorin biyu na Sin da Amurka suna mai da hankali sosai kan dangantakarsu. Muna fatan bangarorin biyu za su yi hangen nesa, domin kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu irin ta hadin kai da juna.'


1 2 3