Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 15:25:41    
Ana kokarin yin amfani da gas a kasar Sin

cri

Ba ma kawai a kauyuka a yi amfni da iskar gas ba har ma a wasu masana'antu.Kamfanin kiwon dabobbi,wani babban kamfani ne na kiwo dabobbi a birnin Lingan na lardin Zhejiang.A da kamfanin nan ya fitar da kashi da sauran tarkacen abubuwa masu dimbin yawa yayin da ake kiwon dabbobi.Wannan ba ma kawai ya kazantar da ruwan dake wuraren kusa da gonakan shimkafa ba,hatta ma ya kawo lahani ga muhallin zaman rayuwa na manoma na wurin.

Domin canza wannan halin da ake ciki,Kamfanin kiwon dabobbi na Zhengxing ya gina ramin iskar gas cikin yin amfani da kashin dabobbi a shekarar bara.Wakilin gidan rediyonmu da ya ziyarci lardin Zhejiang ya bayyana cewa "A kamfanin kiwon dabobbi na Zhenxing,na ga yadda aka sami gas halitta cikin yin amfani da kashin dabobbi,ma'aikatan kamfanin suna dafa abincin da iskar gas da aka samu ta hanyar nan,sa'an nan sun mai da kashin dabobbi takin gida,a kan ba manoma takin gida da ruwan takin ba tare da biyan kudi ba,manoma suna noma shuke shuke da takin da suka samu,daga baya sun sami kararen amfanin gona,su zuba su cikin ramin iskar gas ,lalle kyakkyawar hanya ce ta zaman rayuwar dan Adam.

Bisa labarin da aka bayar,an ce kawo karshen shekarar 2003 an sami ramuka manya da matsakaita kimanin metan a lardin Zhejiang na kasar Sin,an sarrafa kashin dabobbi da sauran tarkace Ton miliyan 2 da dubu dari 8 a shekara,da fitar da iskar gas da ya kai cubic mita miliyan biyar da dubu metan a shekara,ta haka aka samo wata sabuwar hanyar kiwon dabobbi maras lahani da kazantarwa a kasar Sin.


1 2 3