Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 15:25:41    
Ana kokarin yin amfani da gas a kasar Sin

cri

Yankin da birnin Enshi na lardin Hubei ke mallaka yana daya daga cikin yankunan kasar Sin da suke kasancewa jagora wajen yin amfani da iskar gas.Shigar wakilin gidan rediyonmu ya gidan manomi Mista Xiang Yiji ke da wuya,sai ya ga wani bututun leda mai launin fari dake jikin bango ya mika cikin daki daga wani ramin iskar gas a waje da gidan.Da aka bude mabudin fitilar da iskar gas din,nan da nan fitilar ta kunnu,hasken fitila ya game ko ina a dakin.Da aka bude mabudin murhu,sai harshen wuta mai launin shudi ya tashi;da aka bude mabudin abin dumama ruwa,sai nan da nan ruwa mai zafi ya fito.

Mista Xiang Yiji ya bayyana cewa manoman wurin suna da al'adar kiwon aladu.amma ga kashin alade a ko ina saboda rashin kulawa.yau shekaru 5 ke nan da gwamnatin wurin ta yi wa manoma jagora wajen gina ramin iskar gas ,ta samar da taimako na sumunti ga manoma.Matakin nan da aka dauka ya sami karbabuwa daga manoma.Bayan da aka yi gwagwarmya cikin shekarun baya,kashi 70 cikin kashi dari na iyalan manoma sama da 260 na kauyen nan sun gina ramukan iskar gas .Mista Xiang Yiji ya ce wannan ramin iskar gas na sabon salo yana da amfani da dama,ya kan samar da wuta mai kyau.

Mista Xiang Yiji ya ce a da manoman kauyen nan sun dafa abinci ne da kwal da suka saya ko da itatuwa da suka sara,sayen kwal na bukatar kudi,sara itatuwa na lahanta yanayin muhalli,hayakin da aka faitar saboda kone kwal da itatuwa ya kazantar da yanayin wurin.Tea da aka noma a wurin da wuya a sayar da su saboda kanana abubuwa masu lahani da ke ciki.


1 2 3