Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 15:25:41    
Ana kokarin yin amfani da gas a kasar Sin

cri

Iskar gas ba ma kawai ya sami maraba a kuyukan lardin Hube ba,hatta ma ya sami karbabuwa a sauran larduna na kasar Sin.A gidan manoni mista He shiyan a kauyen Chunfeng na gundumar Yueyang ta lardin Hunan,wakilinmu ya ga aladu guda biyu da zomaye fiye da goma da ake kiwo,bai ji wani wari ba a gidan saboda ana zubar da kashin dabobbi cikin ramin iskar gas ,ga fili na da tsabta kuma ba kudaje.Mista He shiyan ya gaya wa wailinmu cewa

"Da farko kashin dabobbi ya zama makamashi,na biyu za a iya noma laiman kwadi da tarkacen kashin,ta haka kudin da manoma za su samu zai karu.An gina ramukan iskar gas sama da talatin a kauyen nan kusan kowane iyali nada ramin iskar gas daya."

Mista He Shiyan ya ce iyalinsa ya dauki nauyin kula da wani lambun itatuwa masu ba da 'ya'ya masu zaki da ake kira "peach"a turance,ba ya amfani da takin zamani,ya yi amfani da tarkacen abubuwan da aka samu daga ramin iskar gas ,'ya'yan itatuwan da ya samu sun fi girma da kyaun gani da kuma dadin ci,farashinsu ma ya dan karu.


1 2 3