Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:45:06    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami kyakkyawan sakamako wajen raya harkokin kasuwanci

cri

A cikin shirin raya harkokin kasuwanci na gasar wasannin Olympic ta Beijing, shirin sayar da kayayyakin da suke da lasisi na musamman ya fi nasaba da fararen hula, saboda wadannan kayayyaki kowa da kowa yana iya ganinsu da taba su da kuma sayensu. Madam Yuan ta kara da cewa, kayayyakin gasar wasannin Olympic ta Beijing da suke da lasisi na musamman suna da iri-iri, a ciki har da kayayyakin tunawa da wasan Olympic masu salon gargajiya da kuma wasu masu sigar musamman ta Beijing da ta kasar Sin. Kazalika kuma, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya gabatar da kayayyakin da aka sayar da su kadan bisa jerin muhimman batutuwa. Wadannan kayayyaki masu daraja ta fuskar fasaha da al'adu sun sanya mutane suna ruguguwa wajen sayensu. A ganin wannan jami'ar kasar Sin, ba a iya raba sayen ribibin kayayyakin wasan Olympic masu daukar lasisi na musamman daga kaunar ra'ayin wasan Olympic da jama'ar Sin da jama'ar ketare suke nunawa da kuma goyon baya da kulawar da suke nunawa kan gasar wasannin Olympic ta Beijing ba. Ta gaya wakilinmu cewa,'Mun yi shirin kafa shagunan musamman na sayar da kayayyakin wasan Olympic a dukan filayen wasa, a ciki kuma har da wani babban kanti mai fadin misalin murabba'in mita dubu 3 a wurin yawon shakatawa na wasan Olympic, ta haka mutane za su kara samun saukin sayen kayayyakin da ke da lasisi na musamman.'

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kiyasta cewa, saboda kusantowar gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma gabatar da sabbin kayayyaki, shi ya sa yawan kayayyakin gasar wasannin Olympic ta Beijing masu daukar lasisi da za a saya zai kara karuwa. Madam Yuan ta yi nuni da cewa, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing zai inganta kula da shagunan sayar da kayayyaki masu daukar lasisi da kuma kyautata matsayinsu na ba da hidima, ta haka dimbin masu saye-saye za su sami kyakkyawan muhalli a fannin yin saye-saye.(Tasallah)


1 2 3