Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:45:06    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing ta sami kyakkyawan sakamako wajen raya harkokin kasuwanci

cri

A halin yanzu, kamfanoni 12 abokan da suka hada gwiwa da kwamitin wasan Olympic ta kasa da kasa suna mara wa gasar wasannin Olympic ta Beijing baya ta fuskar kudade da hidima. Haka kuma, masana'antu 11 na gida da na ketare sun zama abokan da suka hada gwiwa da gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ban da wannan kuma, wasu 9 sun zama wadanda suka ba da kudade wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Bisa halin da ake ciki a yanzu, an sami kyakkyawan sakamako wajen raya harkokin kasuwanci na gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma ana sa ran cewa, kudaden shiga za su wuce makasudin da aka tsara a yayin da ake neman samun bakuncin shirya gasar.

Bisa halin da ake ciki a gun gasannin wasannin Olympic na Beijing da aka yi a da, aikin raya harkokin kasuwanci ba kawai ya iya tattara kudade da kayayyaki da hidimomin da abin ya shafa domin shirya gasar wasannin Olympic ba, har ma ya iya daukaka bunkasuwar masana'antun da suka ba da kudade da kuma yin hadin gwiwa. Gudanar da shirin raya harkokin kasuwanci na gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kyautata tunanin al'ummar Sin na kiyaye ikon mallakar ilmi, ya kuma samar wa masana'antun da suka ba da kudade wajen shirya gasar wasannin Olympic kyakkyawar yanayi a harkokin kasuwanni.


1 2 3