Yanzu an rage kwanaki 160 ko fiye da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008. A matsayinsa na muhimmin bangare na ayyukan shirya gasar wasannin Olympic, raya harkokin kasuwanci na gasar wasannin Olympic ta Beijing ya sami kyakkyawan sakamako.
Ran 20 ga wata, a nan Beijing, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kira taron manema labaru kan ayyukan raya harkokin kasuwanci, inda madam Yuan Bin, shugaban sashen raya harkokin kasuwanci na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta yi karin bayani a wannan fanni. Madam Yuan ta bayyana cewa, tun bayan da aka kaddamar da shirin raya harkokin kasuwanci na gasar wasannin Olympic ta Beijing a watan Satumba na shekarar 2003, har zuwa yanzu kwamitin shirya gasar wasannin Olumpic ta Beijing na tsayawa tsayin daka kan bin manufar 'bude kofa ga kasashen duniya wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing', shi ya sa ayyukan bunkasa harkokin kasuwanni sun jawo hankulan dimbin masana'antun na gida da na waje. Ta ce,'A watan Yuli na shekarar bara, mun kammala tattara masana'antun da suka ba da kudade wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. A sakamakon kaddamar da shirye-shiryen kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya da kuma watsa labari ta telibijin da kuma shirin kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing kan raya harkokin kasuwanci, mun sami isassun kudade da kayayyaki da kuma goyon baya ta fuskar fasaha da hidima domin shiryawa da kuma gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing.'
1 2 3
|