Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:44:02    
Cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini

cri

Wata sabuwa kuma an bayyana cewa, manazarta na jami'ar fasaha ta Cornell ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga cocoa da ke cikin cakulan kan halinsa na musamman wajen kiwon lafiya, daga baya kuma sun gano cewa, wani sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant da ke cikin cocoa ya ninka har sau biyu bisa na jar wine, ya kuma ninka har sau uku bisa na koren shayi wato green tea.

Sinadarin antioxidant yana iya ba da taimako wajen rage saurin yaduwar kwayoyin sankara da kuma shawo kan barkewar sankara, ban da wannan kuma yana iya ba da tasiri wajen yin rigakafin cututtukan zuciya da sauran cututtukan da ke da nasaba da tsufa. A cikin dukkan sinadarin antioxidant, sinadarin polyphenol ya fi kyau. Cocoa yana kunshe da dimbin irin wannan sidanari, inabi da cherry da kuma jar wine su ma suna kunshe da sinadarin.

Ban da wannan kuma manazarta sun yi bayanin cewa, ana iya samun sinadarin ferrum da magnesium da kuma phosphor da yawa a cikin cocoa, kuma bakar cakulan tana kunshe da sinadarin ferrum mafi yawa idan an kwantanta da farar cakulan.(Kande Gao)


1 2 3