Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:44:02    
Cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini

cri

Manazarta na kasar Jamus sun bayar da wani rahoto a cikin mujallar kungiyar aikin likitanci ta kasar Amurka, cewa sakamakon nazari da suka yi ya bayyana cewa, cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini.

Kafin wannan, wani nazarin da aka yi ya taba shaida cewa, sabo da bakar cakulan tana kunshe da sinadarin polyphenols, shi ya sa take iya rage hauhawar jini. Amma wasu kwararru sun nuna damuwa cewa, idan ana cin bakar cakulan da yawa fiye da kima, yawan sukari da kitse da calorie da za a samu zai kawo cikas ga amfanin bakar cakulan wajen rage hauhawar jini.

Sabon nazarin da manazarta na asibitin da ke karkashin jami'ar Koeln ta kasar Jamus suka yi ya tabbatar da cewa, idan ana cin bakar cakulan kadan kamar mai yawan kusan gram 6.3 a ko wace rana, za a iya samun raguwar hauhawar jini ba, kuma ba zai haddasa karuwar nauyin jiki da kuma sauran amfani maras kyau ba.


1 2 3