Manazarta sun gudanar da wannan bincike ga mutane 44 da shekarunsu ya kai 56 zuwa 73 da haihuwa, wadanda dukkansu suke da hauhawar jini a matsayi daban daban, kuma ba su taba yin jiyya ba. A cikin wannan bincike na makwanni 18, an kasa wadannan mutane cikin rukunoni biyu ba tare da yin zabi ba. Mutanen da ke wani rukuni sun ci bakar cakulan gram 6.3 a ko wace rana, yayin da mutanen da ke daya rukunin suka ci farar cakulan wadda ba ta kunshe da sinadarin polyphenols gram 6.3 a ko wace rana. Daga baya kuma sakamakon binciken ya gano cewa, game da wadanda suka ci bakar cakulan, karfin bugun jini nasu na sama ya ragu da millimeter 2.9 bisa ma'aunin bugun jini, yayin da karfin bugun jini na kasa ya ragu da millimeter 1.9, amma karfin bugun jini na wadanda suka ci farar cakulan bai canja ko kadan ba.
Manazarta sun bayyana cewa, ko da yake ba a iya samun raguwar hauhawar jini sosai ta hanyar cin bakar cakulan ba, amma ya fi kyau a mai da hankali a kan sakamakonsa wajen jiyya. Bisa sakamakon nazarin likitancin da aka yi, an ce idan karfin bugun jini na sama ya ragu da millimeter 3, to hadarin mutuwa sakamakon shanyewar jiki zai ragu da kashi 8 cikin dari, haka kuma hadarin mutuwa sakamakon cutar toshewar jijiyoyin jini na zuciya zai ragu da kashi 5 cikin dari. Ban da wannan kuma, cin bakar cakulan kadan a ko wace rana wani abin sauki ne ga mutanen da ke fama da hauhawar jini, ba a bukatar canja al'adarsu wajen cin abinci sosai ba.
1 2 3
|