Bisa labarin da kafofin watsa labaru suka bayar, an ce, a kwanan baya, kungiyar wakilan kasar Amurka ta nuna damuwarta kan ingancin abinci na Beijing, kuma za ta halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing tare da abincinsu. Game da irin wannan batu, madam Xiang Ping, mataimakiyar direktan ofishin ba da hidimomi ga gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing tana ganin cewa, bisa al'adar da aka saba, ba a yarda da kungiyar wakilan kowace kasa da ta shigar da abincinta a cikin unguwar 'yan wasan motsa jiki ta Olympics ba a gun gasannin wasannin motsa jiki ta Olympics da aka shirya. "An dauki wannan mataki ne domin tabbatar da ingancin abinci. Domin wasu abinci, kamar su danyun abinci, ana bukatar sharuda masu tsanani wajen adana su, amma a cikin unguwar 'yan wasan motsa jiki ta Olympics, babu irin wadannan sharudan da ake bukata. Idan 'yan wasan motsa jiki sun ci irin wannan abinci, za a kawo illa ga lafiyarsu. A waje daya kuma, kowace kasa wadda ke shirya gasar za ta samar da wadatattun abinci a cikin unguwar 'yan wasan motsa jiki ta Olympics. Muna fatan dukkan 'yan wasan motsa jiki za su ji dadin wadannnan abinci."
Amma kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing bai iya sa ido kan ingancin abinci a sauran wurare ba ban da unguwar 'yan wasan motsa jiki ta Olympics. Amma madam Xiang Ping ta nuna cewa, hukumar kwastan ta kowace kasa tana da ka'idoji masu tsanani kan abincin da ake shigi da ficinsu. Ya kamata kungiyoyin wakilai da suke da shirin daukar abinci da kansu su mai da hankulansu kan irin wadannan ka'idoji. A matsayinsu na mai masaukin gasar, kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta birnin Beijing yana fatan kowace kungiyar wakilai za ta yi watsi da irin wannan shiri. Ba ma kawai kasar Sin tana abinci iri iri masu kamshi ba, har ma suna da inganci sosai. 1 2 3
|