Saurari
Ana mai da hankali sosai kan abincin da za a samar wa wadanda za su halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a karo na 29 da za a yi a nan birnin Beijing a lokacin zafi na shekarar 2008. Sabo da haka, yau, wato ran 21 ga wata da safe, gwamnatin birnin Beijing da jami'an kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Beijing sun bayyana cewa, za a tabbatar da ingancin abincin da za a samar a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing.
Madam Tang Yunhua, kakakin ofishin tabbatar da ingancin abinci na Beijing ta ce, "Za mu tabbatar da ingancin abinci ne tun daga asalinsu, wato za mu sa ido kan yadda ake noman hatsi da kiwon dabbobi da yadda ake amfani da magunguna da samar da abincin dabbobi domin tabbatar da ba za a kara magungunan da ba a bukata ba. Sabo da haka, za a iya tabbatar da ingancin abinci, musamman ingancin nama iri iri daga asalinsu."
1 2 3
|