A waje daya kuma, wani jami'in gwamnatin birnin Beijing ya nuna cewa, "ka'idojin tabbatar da ingancin abinci na babban birnin kasar Sin" sun fi ka'idojin tabbatar da ingancin abinci da ake bi a duniya tsanani. Mr. Lu Yong, shugaban cibiyar sa ido kan ingancin abinci na birnin Beijing ya ba da wasu misalai, inda ya ce, "Alal misali, a cikin jikin dabbobi, akwai maganin gina jiki. Bisa ka'idojinmu, ba za a iya samun irin wannan magani ba lokacin da ake binciken ingancin nama. Amma, wasu kasashe sun kayyade yawan irin maganin gina jiki da za a iya samu a cikin nama kawai, kuma irin wannan ma'auni ya yi yawa."
Sabo da haka, jami'ai wadanda suke kula da ingancin abinci a birnin Beijing sun kirayi kungiyoyin wakilan kasashe da yankuna daban daba da masu yawon shakatawa da su kwantar da hankulansu lokacin da suke dandana abincin kasar Sin a nan birnin Beijing.
1 2 3
|