Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:58:15    
An samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a

cri

Madam Ban Li ta ce a cikin shirin samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a ba ma kawai aka samar da kudin taimako ba, har ma an fadakar da kan jama'a kan rawar da suke takawa a zamantakewa da kuma yadda tunaninsu ya dace da muhalli da kuma cusa musu ra'ayin gaskiya na "ka cude ni in cude ka" a zukatansu. Daga cikin dalibai yan mata sama da dubu biyu da suka samu tallafin kudi na shirin, dari takwas ko fiye sun kammala karatunsu a jami'a, sun kuma samu guraban aikin yi. Bisa wata ka'idar da aka tsara a cikin shirin samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a, duk wata dalibar da ta kammala karatunta na jami'a tare da kudin taimako na shirin ya kamata ta taimaka wa wata daliba daga iyali mai talauci da kudi a cikin shekaru biyar bayan ta soke karatu a jami'a idan sharudansu na kudin sun isa matsayin da ake bukata. 'Yan matan da yawa da suka samu aikin yi bayan karatunsu a jami'a sun fara ba da tallafin kudi ga wadanda suke bukata.

A cikin shekaru 12 da suka gabata tun lokacin da aka fara aiwatar da shirin samar da tallafi ga 'yan matan dake karatu a jami'a, shirin nan ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa yammacin kasa da kuma daukaka ci gaban mata, har ma ya zama wani sabon salo na samar da ilimi mai zurfi ga mata a yankuna masu fama da talauci ta hanyar tattara kudi daga jama'a da kuma dogaro bisa albarkatan wuri. A shekara ta 2006 aka mai da shirin samar da tallafi ga 'yan matan da ke karatu a jami'a shirin na farko na ba da misalin koyon da kowa da kowa ya cimma moriyarsa a kasar Sin.

Kan ci gaban da aka samu a cikin shirin samar da tallafi ga 'yan matan dake karatu a jami'a, madam Ban Li ya ce,

"kan makomar shirin samar da talafi ga 'yan matan dake karatu a jami'a, a cikin shekarun baya mun sabunta wasu tsare tsare da yin bincike mai zurfi, za mu kara inganta shirin nan ta hanyar kyautata tsarin tattara kudade da na ba da hidima da mayar da martani ta yadda za mu kara bauta wa jama'ar kasa.(Ali)


1 2 3