Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:58:15    
An samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a

cri

Kusan a ce kowa da kowa na so shiga jami'a domin karo ilimi. Amma ga daliban da suka fito daga iyalai masu fama da talauci, kudin makaranta, babbar matsala ce zuwa gare su. Domin taimakawa wadannan daliban da suka zo daga iyalai matalauta, gwamnatin kasar Sin ta dauki ta dauki matakai da dama, alal misali a rage wani kashin kudin makaranta, ko a ba da rancen kudi ga dalibai. Gwamnatocin wasu birane da larduna na kasar Sin su ma sun ba da nasu tallafi ga daliban dake karatu a jami'a bisa halin da suke ciki. Lardin Shaanxi yana yammacin kasar Sin na tsakiya ya kaddamar da wani shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a. kwanakin baya wakilin gidan rediyonmu ya kai ziyara ga ofishin kula da shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a na hadaddiyar kungiyar mata ta gwamnatin lardin Shaanxi,ya yi hira da madam Ban Li, shugabar ofishin kan yadda aka tafiyar da shirin.

An ce an kaddamar da shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a ne tun daga shekara ta 1996. Hadaddiyar kungiyar mata ta lardin Shaanxi ce ta samar da kudin tallafi na tafiyar da shirin bayan ta sayar da wani zane mai daraja sosai da aka shirya domin taron duniya a karo na hudu na mata.Madam Ban Li ta yi mana bayani kan yadda aka kaddamar da shirin.

"An kaddamar da shirin nan ne domin taimakawa 'yan mata da suka fita daga iyalai masu fama da talaci wajen cika burinsu na shiga manyan makarantu na kasar Sin. Bayar da tallafi wajen samar da ilimi yana da muhimmancin gaske, domin ta haka aka samu kwararrun da za su iya ba da taimakonsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ba kamar yadda aka yi a sauran fannoni ba. "


1 2 3