Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:58:15    
An samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a

cri

Lardin Shaanxi wani lardi ne a baya yake wajen bunkasa tattalin arziki. Yayin da aka fara tafiyar da shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a, kashi biyu bisa kashi uku na daukacin gundumomi na lardin Shaanxi, gundumomin ne da ke fama da talauci. Kudin da ake bukata wajen karo ilimi a jami'a ya kasance babban nauyi ne ga iyalansu musamman iyalai masu fama da talauci a yankunan karkara na lardin. 'yan mata sun fi takwarorinsu maza shan wuya wajen samun kudin makaranta saboda bambance-bambancen da ke kasancewa tsakanin maza da mata a zahiri. Madam ta ci gaba da cewa a wuraren da dama a lardin Shaanxi,idan yaro da yarinya daga iyali daya dake fama da talauci suka ci jarrabawar shiga jami'a, iyalin ya samar da kudin makaranta ga yaro kawai, yarinyar ta kan rasa damar shiga jami'a, sabo da kudin makarantansu ya gagari iyali mai talauci. Da ganin haka, hadaddiyar kungiyar mata ta lardin Shaanxi, a kan matsayinta na kungiyar dake wakiltar mata da kare moriyarsu, ta kaddamar da shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a.

Bayan da aka aiwatar da shirin ba da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a, an samar da kudin taimako da ya wuce kudin Sin Renminbi Yuan miliyan takwas da dubu dari shida ga dalibai 'yan mata fiye da dubu biyu daga iyalai masu fama da talauci. Wadannan kudin taimakon sun zo ne daga hukumomin kasa da kasa, da asusun samar da ilimi da kuma mutanen da suka ba da taimako.Madam Ban Li ta ci gaba da cewa

" Farar hula ne suka nuna kaunarsu wajen samar da kudin taimako na tafiyar da shirin samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a. Irin shirye-shiryen ya fi samu amincewa daga jama'a, jama'a masu tarin yawa ma su kan ba da tallafinsu. "

An sami labarai da dama wadanda suka girgiza zukatan jama'a na game da ba da tallafin kudi yayin da ake tabbatar da shirin samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a. Wani mutumin mai ba da taimakon kudin da ake kiransa Zhang Liren ya ba da kudin taimko ga 'yan mata daga iyalai masu fama da talauci cikin dogon lokaci, daga baya ya kamu da ciwon kan jiki, matarsa ma ta rasa aikin yi. Domin kudin da yake bukata wajen samun magani ya yi yawa, ofishin kula da shirin na lallashi shi kada ya ci gaba da ba da taimakon kudi, amma ba ya so ya yi watsi da haka, ya ci gaba da ba da taimakon kudi cikin shekaru biyar har zuwa ranar da ya rasu. Daga bisani aka yi masa lakabi "jakada mai nuna kauna" na shirin samar da tallafi ga 'yan mata dake karatu a jami'a.


1 2 3