Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:55:23    
Jihar Ningxia tana samun saurin bunkasuwar sha'anin abincin Musulmi

cri

"Abincin musulmi abinci na musulmi ne, kuma abincin da duk 'dan Adam ke so. An dauki ka'idojin gyare-gyaren abincin musulmi kamar ma'aunin kiwon lafiya na duniya. Domin kyautata ayyukan gyare-gyaren abincin musulmi, da na fitarwa, a 'yan kwanaki masu zuwa, za a kafa cibiyar ba da shaida ga abincin musulmi ta jihar Ningxia, da kuma cibiyar nazarin fasahar kula da ingancin abincin musulmi na shigi da fici. Wadannan hukumomi biyu za su ba da tabbaci wajen ingancin abincin musulmi."

Yanzu, birnin Yinchuan na jihar Ningxia yana jagoraranci dukkan jihar mai ikon aiwatar da harkokin kanta wajen bunkasa sana'ar abincin musulmi. Yana mayar da karfafa sana'ar musulmi ta zama abu mai muhimmanci wajen daidaita tsarin tattalin arziki. Bugu da kari kuma, ya kafa karmar kungiyar jagorancin harkokin bunkasuwar sana'ar abinci da kayayyakin musulmi ta birnin Yinchuan, ciki har da hukumar sha'anin kudu, da ta al'umma da addinai, da kuma sauran hukumomi guda 16. Bayan haka kuma, tun daga shekarar 2006 har zuwa shekarar 2011, birnin Yinchuan zai zuba kudin Sin RMB miliyan 5 a ko wace shekara, don nuna goyon baya ga masana'antun gyare-gyaren abincin musulmi a fannonin nazarin sabbin kayayyaki, da habaka kasuwa, da horar da kwararru, da dai sauransu, haka kuma ya ba da tabbaci ga saurin bunkasuwar abincin musulmi na birnin Yinchuan na jihar Ningxia a fannonin kudi da kwararru.(Bilkisu)


1 2 3