Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:55:23    
Jihar Ningxia tana samun saurin bunkasuwar sha'anin abincin Musulmi

cri

Bisa kididdigar da aka yi an ce, yanzu akwai musulmi kusan biliyan 1.3 a dukkan duniya. Wadanda daga kasar Sin kuma sun kai sama da miliyan 20, yawancinsu sun taru a jihar Ningxia, da jihar Qinghai, da kuma sauran yankunan da ke yamma maso arewacin kasar Sin. A 'yan shekarun da suka wuce, jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta kara saurin bunkasuwar sana'ar abincin musulmi, sakamakon haka, ba kawai an sayar da abincin musulmi zuwa kasuwar kasar ba, har ma ana ta kara sayar da su zuwa kasuwar kasashen ketare. A cikin shirinmu na yau kuma, bari mu ga bayanin da wakilin sashenmu na Hausa 'Dan Ladi ya ruwaito mana daga jihar Ningxia.

Lambun masana'antu na abincin musulmi na "De Sheng" da ke birnin Yinchuan na jihar Ningxia na iya wakiltar sana'ar abincin musulmi na dukkan sana'ar abincin musulmi ta jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui. Yanzu, masana'antun samar da abincin musulmi da ke cikin lambun ya kai 22, kuma suna fitar da abincin musulmi na musamman, ciki har da abincin naman tunkiya, da na nono, da kuma kyat, da dai sauransu, wadanda ke da halin musamman na wurare daban daban. A shekarar 2007, yawan kudin da lambun masana'antu na abincin musulmi na "De Sheng" ya samu, ya kai kudin Sin RMB miliyan 400, wato ya karu da kashi 35 cikin dari bisa na makamacin lokaci na shekarar 2006. Malam Ma Xing, mai gyara abinci da ke aiki a wannan lambun masana'antu, yana ganin cewa, sai dai ta hanyar samun nasara wajen inganci kawai, za su iya kafa alamar abinci irin ta naman tunkiya ta jihar Ningxia, da kuma kara samun amincewa wajen kayayyakinsu.


1 2 3