Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-21 14:55:23    
Jihar Ningxia tana samun saurin bunkasuwar sha'anin abincin Musulmi

cri

"A kan abincin musulmi, muna bin gargajiya ta musulmi sosai. Mu musulmi muna da fasaharmu wajen gyare-gyaren abinci, muna aiwatar da hasahar sosai. Abincin da muka fitar sun samu karbuwa sosai daga musulmi, da kuma sauran kabilu."

A matsayinta na wata shiyya mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur daya kawai a nan kasar Sin, jihar Ningxia tana da sharuda masu kyau, da kuma fifikon albarkatu wajen bunkasa sana'ar abincin musulmi da kayayyakin musulmi. Bisa labarin da muka samu, an ce, yanzu masana'antun da ke gudanar da ayyukan yin gyare-gyaren abincin musulmi a jihar Ningxia sun kai sama da 540. A shekarar 2007, yawan kudin da jihar ta samu wajen sana'ar musulmi ya kai kudin Sin RMB biliyan 8, ciki kuma yawan kudin da aka samu wajen sana'ar gyare-gyaren abincin musulmi ya kai kudin Sin RMB biliyan 5. Lallai karfafa bunkasa sana'ar abincin musulmi da kayayyakin musulmi, wannan wani muhimmin mataki ne da aka dauka wajen bunkasa tattalin arzikin al'umma, da kara matsayin kawo albarkatu da zaman rayuwar 'yan kananan kabilu, da kuma sa kaimi ga dauwamammen cigaban tattalin arziki na jihar Ningxia kamar yadda ya kamata.

Domin karfafa yin cudanya da hadin gwiwa tare da masana'antun gyare-gyaren abincin musulmi na kasashen ketare, da kuma kara jawo hankulan 'yan kasuwa baki da su zuba jari a jihar Ningxia. Jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta shirya bikin abincin da kayayyakin musulmi, wanda ya jawo hankulan 'yan kasuwa na gida da na waje da yawa. Madam Ma Fengxia, wata jami'ar sashen tattalin arziki na kwamitin kula da harkokin al'umma na jihar Ningxia, ta ce,


1 2 3