Biran da su kan yi wasa da juna su kan faranta wa masu yawon shakatawa rai. Har ma mutane da yawa ba su son komawa gida. Amma ina dalilin da ya sa wadannan birai suka zo nan daga manyan tsaunukan Taihangshan, sun kuma saba da muhallin wurin, inda suke jin dadin zamansu? Mun sami dalili daga malama Wang Jianping, wadda ke kiwon biran. Ta ce,
'Matarin ruwa na tabkin Nanwanshu ya dace da birai sosai saboda muhalli mai kyau da kuma tsire-tsire masu yawa. Akwai itatuwa iri daban daban masu tarin yawa a wajen, wadanda tsawon shekarunsu ya wuce dari daya ko kuma dubu 1. Ana samun itace masu ba da chestnut irin na kasar Sin, biran suna son cin chestnut irin na kasar Sin kwarai. Sa'an nan kuma, akwai itatuwa masu yawa da biran suke son cin 'ya'yansu a manyan duwatsu. Shi ya sa wurinmu ya cancanci zaman biran sosai.'
Game da al'adun shayi na Xinyang, mazaunan wurin sun ji alfahari sun gaya mana cewa, ganyayen shayi na Xinyang ganyayen shayi ne masu daraja da kuma inganci. Tarihin irin wannan shayi ya kai misalin shekaru dubu 2. Yanzu an sami jerin harkoki game da al'adun shayi a wurin.
To, masu karatu, tabkin Nanwanhu yana maraba da ku domin kai masa ziyara.(Tasallah) 1 2 3
|