Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-19 15:18:12    
Tabkin Nanwanhu a lardin Henan

cri

A cikin dukkan wadannan tsibirai, tsibirin tsuntsaye ya fi yin suna. Ana iya ganin tsuntsaye a ko ina a wajen, haka kuma, ana iya jin kukansu. A watan Maris zuwa na Nuwamba na ko wace shekara, tsuntsayen Egret misalin dubu 100 suna zama a nan daga arewacin kasar Sin a lokacin dari. Abin mamaki shi ne a cikin dukkan tsibirai 61 a tabkin Nanwanhu, don me tsuntsayen Egret suke zama a wannan tsibiri kawai? Dalilin shi ne domin ana samun tsire-tsire masu yawa, musamman ma akwai wani irin ice, wanda ganyayensa su kan samar da kamshin da tsuntsayen Egret suke so, shi ya sa wadannan tsuntsaye masu yawa kamar hakan su kan yi shekarsu a wannan tsibiri. Ban da wannan kuma, ana samun guraba da yawa a wajen, ta haka tsuntsayen Egret sun sami isassun kananan kifaye da jatan lande.

In masu yawon shakatawa sun kawo ziyara ga tsibirin tsuntsaye, to, tabbas ne za su je wurin shakatawa na Niaoyulin mai fadin murabba'in mita dubu 15, inda suke iya ganin tsuntsaye iri-iri fiye da 300 guda dubu 1 ko fiye.

 

Malama Li Ping ta zo tsibirin tsuntsayen daga birnin Beijing domin kallon tsuntsaye, ta gaya mana cewa,

'A kan fi samun dimbin tsuntsayen daji a kan wannan tsibiri. Da yawa daga cikinsu ban san sunayensu ba. Wasu kuma ko a cikin gidan namun daji, ban iya ganinsu ba.'

Bayan da muka bar tsibirin tsuntsaye, mun shiga wani kwale-kwale mai amfani da inji, ba da dadewa ba muka isa tsibirin birai. A kan dogayen itatuwa da bishiyoyi marasa tsayi da kuma a tsakanin duwatsu da ciyayi, biran Macaque sun bullo. Malama Ye, mai jagorantar masu yawon shakatawa ta gaya mana cewa,

'Wadannan biran Macaque sun zo ne daga manyan tsaunukan Taihangshan. Su ne wani iyali. Su na da sarkinsu. Su kan zabi sabon sarki sau daya a ko wadanne shekaru 4. Birai maza masu karfi su kan yi fada mai zafi a tsakaninsu, wanda ya sami nasara zai zama sarkin biran. Sarkin birai yana iya cin abinci kafin saura, kuma yana iya tura sauran birai da su yi tsaron gidansu da neman abinci, kazalika kuma yana iya aurar birai mata masu kyan gani, saura kuwa ba su iya hana shi.'


1 2 3