Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-19 15:18:12    
Tabkin Nanwanhu a lardin Henan

cri

Masu karatu, barkunku da war haka, yanzu lokaci ya yi da za mu fara shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, ni ce Tasallah da mu kan sadu a ko wace ranar Talata. A birnin Xinyang na lardin Henan da ke yankin tsakiya na kasar Sin, akwai wani tabkin Nanwanhu, wanda aka kira shi 'tabki mafi kyan gani a yankin tsakiya na kasar Sin'.

Shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Nanwanhu tana da nisan misalin kilomita 5 a tsakaninta da birnin Xinyang a kudu maso yamma. Ta hada da tabkin Nanwanhu da wurin yawon shakatawa na gandun daji na Nanwan. A kewayen tabkin Nanwanhu, ana iya ganin gandun daji da kuma tsibirai.

 

Baya ga albarkatun gandun daji da dimbin tsibirai da kananan tashoshin jiragen ruwa da kuma muhallin halitta mai kyau, tabkin Nanwanhu ya fi jawo masu yawon shakatawa daga wurare daban daban domin al'adun shayi na Xinyang da kuma al'adu na kifaye na Xinyang. Liu Bin, mataimakin shugaban hukumar kula da shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Nanwanhu ya gaya mana cewa,

'Shiyyarmu ta yawon shakatawa ta tabkin Nanwanhu shiyyar yawon shakatawa ce a matsayin 4A a kasar Sin, kuma shiyyar yawon shakatawa ta kasar ce a harkokin yin amfani da ruwa, ita ce kuma wurin yawon shakatawa na gandun daji na kasar Sin. An dade ana kiranta tabki mafi kyan gani a yankin tsakiya na kasar Sin. Fadin ruwan ya kai misalin murabba'in kilomita 75, fadinsa ya fi tabkin Xihu na birnin Hangzhou sau 11. Ruwan tabkin yana da tsabta sosai. Sa'an nan kuma, yana kasancewa da tsibirai manya da kanana 61 a tabkin. Dukkansu suna da kyan gani ainun.'


1 2 3