Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-15 16:25:24    
Gasar Kacici-Kacici ta Wasannin Olympics

cri

Aminai masu sauraronmu, kamar yadda kuka sani cewa, za a gudanar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi a karo na 29 tsakanin ran 8 zuwa ran 24 ga watan Agusta na shekara mai kamawa a nan birnin Beijing, hedwatar kasar Sin. Domin samar muku da wata kyakkyawar damar kara samun ilmi da kuma sa hannu cikin harkokin gasar wasannin, yau dai mun sanar da ku cewa, tun daga ran 1 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki har zuwa ran 1 ga watan Mayu na shekara mai zuwa, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya kaddamar da wata gasar ka-cici-ka-cici mai ban sha'awa a game da gasar wasannin Olympics na Beijing, wadda ke da lakabi haka : ' Mu hadu A Shekarar 2008'.

Gasar din za ta dauki tsawon watanni shida. A cikin wannan lokaci dai, za mu watsa muku bayanan musamman guda hudu na game da wannan gasa daya bayan daya. Kanun bayani na farko shi ne : ' Ana gudanar da ayyukan share fagen gasar wasannin Olympics na Beijing lami-lafiya' ; Kanun bayani na biyu shi ne : ' Babban take da kuma kayan dake kawo sa'a na gasar wasannin Olympics na Beijing' ; Bayanin musamman na uku na da lakabi kamar haka : ' Bayani kan dakuna da fiyalen wasa na gasar wasannin Olympics ta Beijing' ; Kanun bayani na hudu wato na karshe shi ne : ' Bayani kan biranen da suka bada taimako wajen gudanar da gasar wasannin Olympics na Beijing'.


1 2 3