Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-31 16:57:20    
Tagwaye Faransawa suna zama wani karamin gari na kasar Sin

cri

Daga baki masu yawon shakatawa a Yangsuo, Mr Lue Vin Centa ya samu wata alama,wato kasar Sin mai daddaden tarihi yana nan yana jawo hankulan mutanen duniya."Faransawa da yawa suka yi farin ciki da ziyararsu a kasar Sin. A ganinsu gwamnatin kasar Sin ta yi musu ayyuka da dama. Kashi 95 bisa dari na baki ba su taba tsammanin hakan kasar Sin ke ciki ba. Dukkansu sun ce kasar Sin tana da kyaun gaske. "

Yanzu Mr Lue Vin Cent shi ma yana zama a garin Yangsuo. Ya gano wani ginin tarihi na sigar gargajya mai tsawon shekaru sama da dari uku na dab da dakin cin abincin irin na Faransa da wansa ya kafa,yana so ya kare wannan kyakkyawan wuri da nuna halayensa masu nagarta. Bayan da ya samu goyon baya daga gwamnatin wuri, ya zuba kudin Sin Yuan miliyan daya wajen bude dakin cin abinci na Hongfu. Bisa fasalin da ya tsara da basirarsa, an kayatar da dakin da abubuwan musamman na kasar Sin ta yadda zai iya shaida al'adun kasar Sin na gargajiya.

Ga shi a yau,mutane na kasar Sin da na kasashen ketare da suke yawon shakatawa a wurin Yangsuo sun yi yawa,wurin Yangsuo ya zama kauyen duniya. Ga mutane masu launi da harsuna iri iri suna wuri da kuma shagunan shan giya da kofi da kuma dakunan cin abinci a gefunan titin Xijie. Al'adun kasar Sin da na kasashen yamma sun hadu a nan, an samu wani yanayi da ya hada al'adun Sin da na kasashen waje. A ganin Mr Lue Vin Cent yayin da ake bude kofa ga kasashen waje,kamata ya yi gwamnatin wuri ta mai da hankali wajen kula da muhallin al'adu na wurin. "Yangsuo ya samu babban ci gba wajen yawon shakatawa,wani abu mafi kyau shi ne ya kasance kamar yadda ya yi a da babu sauyi, dalili kuwa shi ne gwamnatin wurin ya sa hankali wajen kiyaye muhalli,wannan abu ne mafi kyau. "

Garin gundumar Yangsuo ya shahara ne a duniya saboda kyawawan lambuna da yanayin zaman kwanciyar hankali cikin lumana da ya ke da su da kuma titin ciniki na gargajiya da haduwar al'adun kasar Sin da na kasashen yamma. Tagwaye faransawa Chiristophe Vin Cent da Lue Vin Cent,su ne wakilan da suka hada al'adun kasa Sin da na kasashen yamma wadanda suke tafiyar da dakunan cin abincin kasar Sin da na kasar Faransa a garin Yangsuo. A shekara ta 2005, garin Yangsuo ya shiga yakin zaben garurruwa mafiya ban sha'awa da nagarta na kasar Sin da gidan telibiji na gwamnatin kasar Sin ya shirya, Mr Christophe Vin Cent ya zama wakilin garin Yangsuo bisa gayyata. Kanensa Mr Lue Vin Cent ya ce sun samu suna a kasar Sin sabo da sun zo yangsuo.

Jama'a masu sauraro,kun dai saurari wani bayanin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya ruwaito mana kan tagwaye faransawa da ke zama a wurin yangsuo na kasar Sin.Wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na zaman rayuwar Sinawa. Mun gode muku saboda kun saurari shirye shiryenmu.(Ali)


1 2 3