Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri namu na zaman rayuwar Sinawa. A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya rubuto mana kan tagwaye Farasawa da suke zama a wani karamin gari na kasar Sin.
Sunayen tagwaye faransawa su ne Christophe Vin Cent da Lue Vin Cent, suna kaunar garin gundumar Yangsuo dake kudancin kasar Sin sosai. A cikin shekaru fiye da goma da suka wuce, tagwaye faransawa suna tafiyar da wani dakin cin abinci irin Faransa da wani dakin cin abinci na kasar Sin a haraba mai sigar gargajiya ta kasar Sin, suna nazarin rubutun kasar Sin da sassaka, sun kasance tsundun cikin al'adun kasar Sin har ba su yi tsammanin koma gida Faransa ba.
A cikin garin Yangsuo da akwai wani titi mai suna Xijie mai tsawon mita dari biyar da aka gina da tubalin dutse, a gefunan titin da akwai wasu baki na ketare da ke zama a wannan wuri. Tagwaye Faransa Chiristophe Vin Cent da Lue Vin Cent sun bude wani dakin cin abincin Sin mai suna Hongfu da wani dakin cin abincin irin Faransa a bakin wannan titin. Dakin cin abincin Hongfu yana bisa wata haraba mai sigar gargajiya ta kasar Sin da ke da tarihi na shekaru sama da dari uku,har wa yau dai harabar ta kasance kamar yadda ta yi a da,a jikin kofar haraba da akwai zane zanen sassaka da fitilu masu launin ja a rataye,dukkansu suna da wani halayen musamman na kasar Sin. Da ka shiga harabar, ka sha ti kuma ka ci abincin irin na kasar Sin,kana jin wani yanayin kasar Sin na gargajiya ya game ko ina.amma masu kula da dakin cin abinci kuwa baki ne na Farnsa, suna iya magana da sinanci sosai Mr Christophe Vin Cent ya bayyana shirinsa na farko na kafa wannan dakin cin abinci a haraba mai sigar gargajiya na kasar Sin.Ya ce "Tunanina na farko shi ne ina so in kare wannan wuri.Me ya sa wannan wuri ya yi shahara a gida da waje, dalili kuwa shi ne yana da al'adun kasar Sin sosai.Me ya sa mu sami suna a wannan gari, domin muna kaunar al'adun kasar Sin.Baki sun zo kasar Sin ne domin kara iliminsu na game da al'adun kasar Sin, sun yi yawon shakatawa a kasar Sin ne domin duba kayayyakin al'adun kasar Sin ba domin sabbin gine ginen da aka girka ba."
An kayatar da dakin cin abinci Hongfue ne bisa fasalin da Lue Vin Cent ya tsara. A jikin kofofi da tagogi an sassaka zane zanen dragon da phoenix wadanda suka alamanta al'adun kasar Sin dake da nufin zaman jin dadi. Sunan dakin cin abinci Hongfu yana nufin ka sami sa'a da dama. Tagwaye faransawa ma suna da sunayen sinanci wato "shuangfu" da "Shuanglu",ma'anar sinanci ma "samu sa'a". Daga nan da sauki za ka iya gane tagwaye faransa sun sami tasiri daga al'adun kasar Sin,suna kaunar al'adun kasar Sin Wannan shi ne dalilin da ya sa sun zo nan kasar Sin."
Mr Lue Vin Cent ya ce "tun lokacin da muke kanana daga firamare zuwa jami'a, muna so mu yi koyi da tarihin kasar Sin da al'adunta. A kasar Faransa ina tsammanin kasar Sin kasa ce mai girma, tana da tarihi na shekaru sama da dubu biyar. Abu na farko da na samu labari na dangane da kasar Sin shi ne sinima. Muna mafarkin zuwa kasar Sin,muna kaunar wannan wuri tun isowarmu. "
Tagwaye faransawa an haife su ne a birnin Strasbourg, shahararren birnin tarihi da al'adu da ke arewa maso gabashin kasar Faransa. Mr Christophe Vin Cent yana so ayyuka masu cike da kasada tun yana karami. A shekara ta 1988 ya shiga rundunar soja da aka tura shi zuwa jamhuriyar Gabon ta Afrika.Wannan tarihi ya bude idanunsa. Bayan shekaru biyu ya yi ritaya daga rundunar soja ya zama dan sanda,duk da haka yana so yawon shakatawa a duniya,bi da bi ya yi yawon shakatawa a kasashe 15 na duniya. A shekara ta 1991,tare da kudin da ya tara Mr Christphe mai shekaru 22 ya zo nan kasar Sin musamman domin cika mafarkin gabas da rike da shi cikin shekaru da dama. Ya yi yawon shakatawa daga kudancin kasar Sin zuwa arewancinta, yaziyarci Hongkong,cibiyar kudade ta duniya da ta abinci mai dadi, da babban birni Shanghai wajen tattalin arziki da babban birnin Sin Beijing, cibiyar siyasa da al'adun kasar Sin da shahararrun birane na tarihi Lanzhou da Xi'an dake arewa maso yammacin kasar Sin. Bayan da ya zagaya wadannan wurare masu ban al'ajabi, ya zabi garin gundumar Yangsuo dake kudancin kasar Sin ya tsugunar da kansa a ciki saboda kaunarsa.
1 2 3
|