Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-31 16:57:20    
Tagwaye Faransawa suna zama wani karamin gari na kasar Sin

cri

Gundumar Yangsuo tana karkashin mallakar birnin Guilin na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta inda akwai duwatsu masu ban mamaki da ruwaye masu shudi sosai da garurruwan gargajiya da suke kasancewa cikin kyakkyawan shiri ,za ka iya ga mutanen wuri suna zama cikin yanayin lumana a lambuna. Mr Christophe ya tsungunar da shi a wannan wuri ne sabo da ya tabbatar da mafarkinsa game da kasar Sin na zamanin da. ya ce "ya kosa da zaman faransa, ba ya sha'awar zaman jin dadi, yana kaunar zama na musamman. Ina farin ciki da zama a wannan garin."

Tun daga shekara ta 1993 da Mr Christophe Vin Cent ya tsungunar da shi a garin Yangsuo,shi bai bar wannan garin ba.Wannan namijin da ya zo daga kasar Faramsa mai ban sha'awa ya sami bakin rayuwarsa a wannan karamin gari a gabas mai nesa. Da ya ga bakin da suka zo garin Yangsuo sai kara yawa suke a kwana a tashi, ya samu tunann buda wani dakin cin abincin irin Faransa. Duk da haka kafa dakin cin abincin irin faransa ba aiki mai sauki ba ga Mr Christophe, domin babu danyun kayayyaki da masarufi iri na Faransa a wuri.Amma a halin yanzu jihar Guangxi ta samu babban ci gaba wajen hanyoyiin tafiye tafiya da manyan ayyuka saboda gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufoffi da dama na raya kasa. A kan matsayin bako, Mr Christophe ya ci gajiyar manufoffin, cikin sauki ya tafiyar da dakin cin abincin irin na Faransa.ya kuma gayyaci danesa da ya zo wurin Yangsuo na kasar Sin domin yin ziyara."Da na ke a Afrika,wana ya bar Afrika. Daga baya na tambaye shi ina ya ke? Ya ce yana wani karami gari na kasar Sin da ake kira Yangsuo,wuri ne mai kyaun gani. Ya ce ya iske wani wuri mai kyaun gani, kamata ya yi ka kai ziyara. "

Mr Lue Vin Cent shi ma ya yi aikin soja a Afrika kamar wansa. Daga baya ya yi aiki wani babban kamfani, ya samu albashi mai tsoka. Da ya ga wansa yana kasar Sin ba ya koma gida, shi ma ya kuduri aniyar ziyarar kasar Sin. Daga shekara ta 1995 zuwa shekara ta 1998, ya kai ziyara a kasar Sin har sau uku, abin da ya ganam idanunsa ya sha bambam a ko wane karo."A karo na farko da na isa wurin Yangsuo,wurin ya kasance cikin talauci. bakin da suke zama nan ba su da kudi. Ga shi a yanzu mutanen sun yi yawa,baki masu yawon shakatawa ma suna kara karuwa, da akwai masaukan baki masu taurari hudu ko biyar, lalle an samu manyan sauye sauye a wannan wurin."

1 2 3