Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-04 13:03:53    
Ana fargaban makomar mulkin kasar Burtaniya sakamakon raguwar magoya bayan Mr. Brown

cri

Manufar yaki da ta'addanci da gwamnatin Brown ke aiwatarwa ta janyo kiyayya daga fannoni daban-daban na kasar. Bisa wannan hali dai, Mr. Brown na kokarin samun amincewa da dokar yaki da ta'addanci a majalisar dokokin kasar da zummar tsawaita lokacin tsare wadanda ake tuhumarsu da aikata laifuffuka zuwa kwanaki 42 ba tare da an shigar da kararraki ba. Amma dimbin al'ummomi da kuma wasu masu kare hakkin bil adama na kasar sun yi watsi da yin haka.

Masharhanta sun bayyana ra'ayinsu cewa, bisa hakikanin halin da ake ciki yanzu a kasar Burtaniya, idan gwamnatin Brown tana so ta fitar da kanta daga cikin halin tsaka mai wuya da mua sake samun goyon baya daga 'yan kasar, to ya zama dole ta gudana da harkokin tattalin arzikin kasar da kyau a sabuwar shekara, ta yadda al'ummomin kasar za su ci gajiyar lamarin. ( Sani Wang )


1 2 3