Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-04 13:03:53    
Ana fargaban makomar mulkin kasar Burtaniya sakamakon raguwar magoya bayan Mr. Brown

cri

Sakamakon jin ra'ayoyin jama'a da wasu hukumomi guda shida na kasar Burtaniya suka yi kwanan baya bada dadewa ba na nuna cewa, yawan magoya bayan Jam'iyyar Labour Party dake rike da mulkin kasar Burtaniya a shekarar 2007 ya yi kasa da na jam'iyyar adawa mafi girma a kasar wato Jam'iyyar Commonwealth Party da kashi 9 cikin kashi 100. Wasu masharhanta sun fadi cewa, lallai ba a iya sa ran alheri ga makomar mulkin firaministan Burtaniya Mr.Gordon Brown ta shekara mai kamawa saboda matsin lamba domin kuwa ana sassanta saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar kuma abun kunya na dabaibaye Jam'iyyar Labour Party yayin da ake kalubalantar manufar yaki da ta'addanci da gwamnatin Brown ke aiwatarwa.

Jaridar da ake kira " The Independent" ta Burtaniya ta bayar da wani labarin cewa, sakamakon jin ra'ayoyin bainal jama'a da aka yi na nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, matsakaicin yawan magoya baya da Jam'iyyar Commonwealth Party ta samu ya rigaya ya kai kashi 41cikin kashi 100, amma kuwa kashi 32 cikin 100 ne kacal Jam'iyyar Labour Party ta samu.Wasu manazarta sun yi kiyasin cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa gwamnatin Brown ta samu raguwar magoya bayanta shi ne domin an rage saurin bunkasuwar tattalin arzikin Burtaniya kuma al'ummomin kasar sun nuna rashin amincewa da karfin da gwamnatin kasar take da shi na daidaita batun tattalin arzikin kasar.

1 2 3