
Idan ba a manta ba, gwamnatin Jam'iyyar Labour Party ta taba yin alfarma da karfin da take da shi na gudanar da harkokin tattalih arzikin kasar, amma al'mmomin kasar na shakkar irin wannan karfin da take da shi sakamakon rikicin rancen kudi da ya barke a duniya da kuma tabarbarewar yanayin kasuwannin hada-hadar cinikin gidaje.
Jama'a masu sauraro, yayin da Mr. Brown yake nuna fatan alheri a albarkacin sabuwar shekara ya furta cewa ingataccen tushen tattalin arzikin Burtaniya da kuma babbar manufar gwamnatin kasar, tubali ne mai iganci da zai taimaka wa Burtaniya wajen kawar da tabarbarewar yanayin tattalin arziki a shekarar 2008. Amma wasu kwararru a fannin tattalin arziki na Burtaniya sun yi hasashen cewa, shekarar 2008 za ta kasance wata shekara ce da Burtaniya ta fi samun mummunan yanayin tattalin arziki. Ban da wannan kuma, akasarin al'ummomin kasar Burtaniya su ma suna dauka cewa, lallai gwamnatin Brown na gazawa wajen daidaita batun tabarbarewar tattalin arzikin kasar. Dadin dadawa, kashi uku bisa kashi hudu na kamfanonin kasar sun nuna bacin ransu ga makomar yunkurin bunkasa tattalin arzikin Burtaniya a sabuwar shekara.
Ban da musabbabin tattalin arziki, janyewar Mr. Brown daga babban zaben da aka shirya gudanarwa kafin kayyadadden lokaci, da aukuwar abun kunya na bada kyautar kudi cikin jam'iyyar Labour Party da kuma bacewar bayanai na 'yan kasar Burtaniya da yawansu ya kai miliyan ashirin da biyar da dai sauransu duk sun janyo tasiri ga martabar Mr. Brown da kuma jam'iyyar Labour Party dake karkashin jagorancinsa a cikin zukatan jama'ar kasar. An labarta cewa, za a gudanar da bincike kan abun kunya na bada kyautar kudi; yanzu dai tsohon sakatare-janar na jam'iyyar din yana fuskantar tuhumar aikata danyen aikin. Ko shakka babu wannan lama'I zai ci gaba da dabaibaye Mr. Brown a sabuwar shekara.
1 2 3
|