Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-11 22:03:47    
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bude kofarta ga al'umma domin wasan Olympic

cri

Bugu da kari kuma, a matsayin jadakan kasar da za ta dauki bakuncin gasar wasannin Olympic mai zuwa, Mr. William Geoaffrey Ehrman, jakadan kasar Birtaniya a kasar Sin ya kawo wa ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ziyara a ran 25 ga watan Nuwamba. Wannan jakada ya ce, kasarsa tana alla-alla wajen koyon fasahohin Beijing a fannin samun nasarar shirya gasar wasannnin Olympic. Kwamitocin shirya gasar wasannin Olympic na London da Beijing sun kulla kyakkyawar hulda a tsakaninsu, gasar wasannin Olympic na matsayin wani batu da gwamnatocin kasashen 2 suka sha tattaunawa a kai.

Liu Jia, wani dalibi da ke karatu a kwalejin nazarin hulda a tsakanin kasa da kasa na jami'ar Beijing, ya bayyana ra'ayinsa a madadin wadanda suka kawo wa ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ziyara a wannan rana. Ya ce,'Yau na yi farin ciki sosai saboda kawo wa ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ziyara a ranar da ta bude kofarta ga al'umma. A matsayin wani dalibi, ni ma na zama mai aikin sa kai cikin himma. A shekara mai zuwa da ake yin gasar wasannin Olympic, dakin wasan kwallon tebur na cikin jami'ar Beijing, mu dalibai da malaman koyarwa sun ji matukar farin ciki saboda shiga ciki. Gasar wasannin Olympic wata kasaitacciyar harka ce ga kasar Sin a harkokin diplomasiyya. Ko wane Basinne ya sami damar gudanar da wannan manzanci mai girma, wato gudanar da harkokin waje a tsakanin al'umma.'(Tasallah)


1 2 3