Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-11 22:03:47    
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bude kofarta ga al'umma domin wasan Olympic

cri

Mr. Yang Jiechi ya bayyana cewa, gasar wasanni Olympic na da dankon hulda a tsakaninta da harkokin waje na kasar Sin. Makasudin wasan Olympic da kuma ainihinsa sun zo daidai da babban taken zamaninmu na yanzu, wato wanzar da zaman lafiya da neman samun bunkasuwa, haka kuma sun yi daidai da makasudin kasar Sin na sa kaimi kan raya duniya mai zaman lafiya da wadata har abada. Ya ce,'Gasar wasannin Olympic wani shagali ne mafi girma a duk duniya ta fuskar nuna wasannin motsa jiki da al'adu, a sa'i daya kuma, ita ce wani muhimmin aikin diplomasiyya ga kasarmu. A ganina, wajibi ne mu nuna burinmu na neman zaman lafiya da dimokuradiyya da wayin kai da kuma bude kofa ga kasashen waje cikin jituwa. Sa'an nan kuma, ya zama wajibi mu yi amfani da wannan dama domin inganta zumunci a tsakaninmu da kasashen ketare. Gasar wasannin Olympic na matsayin wata kyakkyawar dama ce wajen yin mu'amala.'

Dadin dadawa kuma, jami'an sashen watsa labaru da sashen kula da harkokin kasashen ketare na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da sashen yada labaru na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun yi karin bayani kan ayyukan harkokin waje na kasar Sin da kuma ayyukan share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing, sun kuma amsa tambayoyin da aka yi masa. Mr. Liu Jianchao, shugaban sashen yada labaru na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ce,'Mun mayar da gasar wasannin Olympic a matsayin wani shagali da wani dandamali ne inda jama'ar Sin da jama'ar duniya za su yi mu'amala a tsakaninsu. A zahiri kuma, gasar wasannin Olympic na matsayin wata kyakkyawar dama. Dukkan mutanen Sin biliyan 1.3 suna alla-alla tare da zura ido kan wannan kasaitacciyar gasa. Bugu da kari kuma, wannan muhimmiyar gasa na kasancewa tamkar wata muhimmiyar dama a gare mu wajen sa kaimi kan ayyukan diplomasiyya da kuma kyautata fahimtar juna da zumunci a tsakanin kasarmu da kasashen duniya. Sa'an nan kuma, mun yi farin ciki sosai saboda muna kokari tare da kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma dukkan mutanen Sin domin tabbatar da samun nasarar kiran wannan gasa.'

Madam Deng Yaping, zakarar gasar wasannin Olympic, kuma mambar kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta kawo wa ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ziyara a karo na farko, ta yi zumudi sosai. Ta ce,'Gudanar da harkokin diplomasiyya ta fuskar wasannin motsa jiki wani muhimmin bangare ne na ayyukan diplomasiyya a tsakanin al'umma. Ina fatan za a kyautata fahimtar juna da zumunci a tsakanin al'ummomi ta hanyar kokarin da muke yi. Babu iyakar kasa a wasannin motsa jiki. Kowa da kowa ya iya fahimtar juna ta hanyar shiga gasa ba tare da wani harshe ba. Shiga gasanni hanya ce mafi sauki wajen yin mu'amala.'


1 2 3