Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 16:18:17    
Shan kofi zai ba da taimako ga lafiyar jikin dan Adam

cri

Ban da wannan kuma a cikin rahoton, an bayyana cewa, an riga an gano cewa, akwai wani sanadari a cikin kofi da ke iya magance cutar hanta sakamakon shan giya, amma ba a gano takamaiman wannan sinadari ba. Bugu da kari kuma, Shan kofi tare da kirim da madara da sukari da sauran abubuwa da 'yan kasar Amurka su kan sanya cikin kofi yana ya ba da taimako sosai ga lafiyar jikinsu.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ta sauran nazarin da aka gudanar kan wannan lamari, an kiyasta cewa, watalika sinadarin da ke cikin Kofi wanda ke ba da taimako wajen kare hanta shi ne caffein. Amma a cikin nazarin, ba a gano cewa, shan shayi zai ba da taimako wajen kare hanta ba, sabo da caffein da ke cikin shayi ya yi kadan idan an kwatanta shi da wanda ke cikin kofi.

A waje daya kuma manazarta sun nuna cewa, ba dukkan mutane masu shan giya za su iya kamuwa da ciwon hanta ba. Ko da yake shan kofi zai ba da taimako wajen kare hanta, amma dabara mafi kyau wajen magance cutar hanta sakamakon shan giya ita ce shan giya kadan ko kuma a daina shan giya sam a maimakon shan kofi da yawa.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka a madadin Kande wadda ke fassara bayanin, ni Lawal nake cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)


1 2 3