Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 16:18:17    
Shan kofi zai ba da taimako ga lafiyar jikin dan Adam

cri

Bisa sabon nazarin da aka yi, masu ilmin kimiyya sun gano cewa, wanda ya kan sha kofi ya fi saukin karbar ra'ayoyin sauran mutane da suka gabatar. Ko mene ne dalilin? Ko sabo da idan an sha kofi, sai za a ji farin ciki? A'a, ba haka ba ne, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan an sha kofi, to harkokin kwakwalwa suna gudana sosai tare da kallafa rai.

Bisa labarin da muka samu daga mujallar Sabbin Masu Ilmin Kimiyya ta kasar Birtaniya, an ce, manazarta na jami'ar Queensland ta kasar Australia sun bayyana cewa, wanda ya kan sha kofi yadda ya kamata ya fi saukin karbar ra'ayin da ya sha bamban da nasa. Don me? Sabo da bayan da aka sha kofi, zai ji farin ciki? Ko akwai sauran dalilai?

Domin fahimtar batun, manazarta sun yi wa mutane 150 jarrabawa. Da farko, an yi musu wasu tambayoyi masu muhimmanci sosai kamar ko suna so a yi musu allurar mutuwa idan su kamu da ciwon da ba a iya warkewa ba ko a'a, daga baya kuma an ba su abin sha iri biyu, daya shi ne abin sha da ke hade da caffein milligram 200, saura dayan kuwa abin sha maras caffein. Bayan mintoci 40, wato lokacin da yawan caffein da ke cikin jininsu ya fi yawa, an gaya musu wasu ra'ayoyin da suka sha bamban da nasu. A karshe dai an gano cewa, mutanen da suke sha abin sha da ke hade da caffein sun fi saukin karbar ra'ayoyi na sauran mutane.


1 2 3