Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 16:16:08    
Bikin nuna wasannin fasahar gargajiya na tsakanin kasa da kasa a kasar Sin ya sa kaimi ga yin ma'amalar al'adu a tsakanin jama'ar kasashe daban daban

cri

Don kiyaye wadannan wasannin fasahohin gargajiya da na kabilu iri iri, gamayyar kasa da kasa sun dauki matakai da yawa. A shekarar 1989, kungiyar UNESCO ta Majalisar Dinkin duniya ta zartas da sanarwar dangane da al'adu iri iri da yawa na kasashen duniya, a shekarar 2003, ta ci gaba da zartas da yarjejeniyar kiyaye abubuwan tarihi na al'adu ba na kayayyaki ba, inda aka karfafa kan muhimmancin kiyaye abubuwan tarihi na al'adu ba na kayayyaki ba, ciki har da wasannin fasahohin gargajiya, wadannan matakai na da amfani ga sa kaimi ga kasashe daban daban da kabilu daban daban da su kara fahimfar junansu da yin shawarwari da ma'amala a tsakaninsu a lokacin gudanar da ayyukan raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya da gyare-gyaren da aka samu a zamantakewar al'umma .

An kafa babbar hedkwatar kungiyar wasannin fasahohin gargajiya na kasa da kasa a kasar Austria, kasashe fiye da 130 suna cikin kungiyar, babbar manufar kungiyar ita ce sa kaimi ga kiyaye wasannin fasahohin gargajiya da kuma shirya tarurukan duniya da nuna wasanni a wurare daban daban na duniya .(Halima)


1 2 3