
Kwanan baya, an rufe bikin nuna wasannin fasahar gargajiya na tsakanin kasa da kasa a kasar Sin. An soma shirya bikin ne a shekarar 1990 don samar da damar musanya da koyi da juna a kan fasahohin nuna wasannin gargajiya a tsakanin 'yan wasannin fasahohi na kasar Sin da na kasashen waje. A gun bikin , masu wasannin fasahohi sun bayyana cewa, ya kamata a raya wasannin fasahohin gargajiya , kuma dole ne su dace da zamanin da muke ciki sa'anan kuma hada da abubuwan zamanin yau da kuma jawo hankulan samarin da za su iya shiga a ciki.
Hadadiyyar kungiyar masu aikin adabi da wasannin fasahohi na kasar Sin ce ta shirya bikin, a shekarar da muke ciki, yawan masu aikin wasannin fasahohi da yawansu ya kai dubu wadanda suka zo ne daga kasashe da jihohi 23 na duniya sun halarci bikin. An shirya bikin a matakai biyu a birnin Suzhou da birnin Beijing wadanda suka yi suna sosai wajen yawon shakatawa a kasar Sin. Wasannin fasahohin da aka nuna sun jawo sha'awa sosai daga wajen masu yawon shakatawa da mazaunan biranen.
1 2 3
|