Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-28 16:16:08    
Bikin nuna wasannin fasahar gargajiya na tsakanin kasa da kasa a kasar Sin ya sa kaimi ga yin ma'amalar al'adu a tsakanin jama'ar kasashe daban daban

cri

Mr George Millor na kungiyar da ake kira "Meccleu Berg Pommeraner Folk Group" ya bayyana cewa, raye-rayen da suka nuna an riga an yadu su cikin daruruwan shekaru a kasarsu, ba ma kawai mutanen kasar Jamus suke son irin raye-raye ba, har ma 'yan kallo na sauran kasashe su ma suna kaunarsu, wannan ne karo na farko da suke nuna raye-rayen a kasar Sin, ya yi farin ciki sosai, ya bayyana cewa, wannan ne raye-raye da wake-wake na wata kabila da suke yaduwa a arewacin kasar Jamus, ya bayyana abubuwan tarihi da labarai da yawa, ya kuma nuna fasahar zamanin da sosai, wasu raye-rayen da aka yi na da tarihin daruruwan shekaru, muna kokari sosai ta yadda raye-rayen kabilarmu suke yaduwa a ko'ina. Muna kan nuna raye-rayenmu a ko'ina a duniya, wannan ne karo na farko da muke zo nan kasar Sin, mun yi mamaki sosai da ganin cewa, an shirya bikin da kyau sosai tare da bin hanyoyi da yawa, muna kaunar wannan wurin.

Mr George ya ci gaba da bayyana cewa, a duk tsawon lokacin bikin, ya taba kallon wasannin fasahohin gargajiya iri daban daban da masu aikin wasannin fasahohin gargajiya na kasashe daban daban suka yi, wasannin fasahohi na kowace kasa na da bambanci da na sauran kasashe, amma dukkansu sun sami abu iri daya gare su, wato sai wasannin fasahohin gargajiyarsu ne za su iya samun karbuwa daga 'yan kallo na sauran kasashe.

A cikin kungiyar kasar Tanzaniya , yawancin masu nuna wasannin fasaha su ne samari, sun nuna wasannin zamani tare da buga gangunan gargajiya, saboda haka sun sami karbuwa sosai daga 'yan kallo, shugaban kungiyar Mr Maurus Wibirili ya bayyana cewa, mun nuna wasanni ta hanyar yin amfani da kayan kida na gargajiyarmu, amma hanyar bugawa da kide-kide su ne na zamanin yau, wannan ya bayyana cewa, a wani fanni, mun gaji al'adar tsofaffinmu, ba mu manta da tarihin kakaninmu ba, amma dole ne mu sami ci gaba, mu yi wasannin fasaha domin samari na zamanin yau, ya kamata mu gaji wadannan kayayyakin kida na gargajiya, kuma mu yada su don buga kide-kide mafiya yawa da kuma bari mutanen sauran kasashe su iya saurarar kide-kidenmu na kasar Tanzaniya.


1 2 3