
Wannan rukunin farko na rundunar aikin injiniya ta kasar Sin ta kiyaye zaman lafiya da yake kunshe da hafsoshi da sojoji 135 sun yi ban kwana da iyalansu da garinsu sun riga sun isa yankin Darfur na kasar Sudan domin sauke nauyin da ke bisa wuyansu. Ko da yake halin da ake ciki a yankin Darfur yana da sarkakiya, amma dukkan sojojin rundunar sun ce,
"Muna alfahari domin za mu sauke nauyin da aka dora mana a madadin kasarmu."
"An ba mu wannan aiki domin an amince da mu."
"Ya kasance da rukunin farko na rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya da ya isa yankin Darfur, nauyin da ke bisa wuyanmu yana da muhimmanci sosai. Za mu sauke nauyin kamar yadda majalisar dinkin duniya ta dora mana domin kafa wani tushe mai inganci ga sauran rundunonin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da za a jibge su a Darfur. Muna fatan za mu taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin Darfur, har ma da na duk duniya." 1 2 3
|